Nasara a Tattalin Arziki: Sama da Kashi 85% na Kanana da Matsakaitan ’Yan Kasuwa sun rungumi Tsarin Biyan Kudin Zamani
Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani ta sanar da cewa an samu gagarumar nasara, inda sama da kashi 85% na kanana da matsakaitan ’yan kasuwa (SMEs).
A Najeriya suka fara amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani, Wannan ci gaba babban mataki ne ga shirin nan na Paperless Nigeria na shekarar 2026, wanda ke nufin rage amfani da takardu da tsabar kudi a harkokin yau da kullum. Wannan nasara na nuna yadda kasar ke saurin sauyawa zuwa tsarin tattalin arziki na na’ura mai kwakwalwa.
Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, ya bayyana cewa wannan nasara ba ta zo cikin sauki ba, sai ta hanyar hadin gwiwa da kamfanonin fasahar kudi kamar su Moniepoint da PalmPay.
Wadannan kamfanoni sun taimaka wajen kai ayyukan banki har zuwa lungu da sako na kasar nan, wanda hakan ya ba wa talaka da masu kananan sana’o’i damar karbar kudi da kuma tura kudi ba tare da sun je banki ba. Wannan ya sa harkar kasuwanci ta zama cikin sauri da kuma aminci.
Shirin Paperless Nigeria wanda ya fara aiki sosai a karkashin wannan gwamnati, na da burin ganin cewa kusan kashi 95% na ’yan Najeriya sun samu ilimin amfani da na’urorin zamani nan da shekarar 2030. Nasarar da aka samu a yau ta SMEs na nufin cewa ’yan kasuwa sun gane amfanin kiyaye bayanan kasuwancinsu a na'ura, wanda hakan ke taimaka musu wajen samun bashi daga bankuna da kuma bunkasa sana’o’insu zuwa mataki na gaba.
Haka kuma, ma’aikatar ta bayyana cewa wannan sauyi ya rage cin hanci da rashawa da kuma bata lokaci a ma’aikatun gwamnati da na kamfanoni. Tun daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026, ma’aikatun gwamnatin tarayya suka koma tsarin aiki ba tare da takarda ba, kuma rungumar wannan tsari da ’yan kasuwa suka yi ya kara karfafa gwiwar gwamnati wajen fadada ayyukan intanet zuwa yankunan karkara.
A karshe, masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa tattalin arzikin zamani na Najeriya zai samar da kudin shiga har dala biliyan 18.3 nan da karshen shekarar 2026.
Rungumar tsarin biyan kudi na zamani da SMEs suka yi zai taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri, wanda hakan zai kara bunkasa darajar kudin kasar da kuma samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa a fadin kasar nan.

Comments
Post a Comment