Kungiyar RACOC Ta Bude Asibitin Wucin Gadi a Rangaza Don Inganta Lafiyar Al'umma


A ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, 2026, kungiyar Rangaza Active For Change The Community (RACOC) ta gudanar da taron tantancewa na wat a kamar yadda aka saba. 

Taron ya sake jaddada kudirin kungiyar na ci gaba da bin diddigin ayyuka da kuma sanya ido kan bukatun al'umma a kowane wata ba tare da ta sha ba.

Bayan kammala taron ne aka kaddamar da asibitin wucin gadi na Primary Healthcare a Unguwar Inkyan Jikin Gidan Alh. Ali Bashir Mai Unguwa, dake Rangaza Cikin Gari a Karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano. 

Wannan mataki ya zo ne a matsayin martani na gaggawa domin magance matsalolin rashin samun kulawar lafiya da maza, mata, yara da manya ke fuskanta a yankin.

Babban makasudin kafa asibitin shi ne saukaka wa jama'a samun magani da kulawar likita ba tare da sun sha wahala ba, musamman ma mata masu juna biyu da ke bukatar kulawa ta musamman. 

Alhamdulillahi, an fara gudanar da ayyuka yadda ya kamata, kuma al'umma sun fara amfana da wannan babbar dama ta lafiya da aka kawo musu kusa da gidajensu.

Daga karshe, shugabancin kungiyar ya mika godiya ta musamman ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudummawar abin duniya, lokaci, lafiya da kuma addu'a wajen ganin an cimma nasarar wannan tsari. 

Kungiyar ta nuna jin dadinta tare da addu'ar Allah Ya saka wa kowa da alkhairi, Ya kuma ci gaba da ba su ikon gudanar da ayyukan alheri da suke yi domun ci gaban al'umma.


Comments

Popular posts from this blog

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Syria: Sabon Matakin Diflomasiyya tsakanin Gwamnati da Mayaƙan Ƙurɗawa

Wani ɗan asalin Ireland ya shiga rikici a wata ƙasa – Gwamnatin Ireland na sa ido kan lamarin

Saudi Arabia da Najeriya Sun Kulla Yarjejeniyar Daukar Ma’aikata