Neymar Ya Amince Cewa Ritaya Ta Kusa Fiye Da Yadda Ake Tsammani
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Neymar Jr, ya girgiza duniyar wasanni ta hanyar bayyana cewa lokacin da zai rataye takalmansa ya kusa.
A cikin wata hira Neymar ya bayyana cewa watan Disamba na wannan shekara na iya zama lokacin da zai yanke shawarar yin ritaya daga fagen ƙwallon ƙafa.
Wannan furuci ya zo ne a daidai lokacin da magoya baya ke fatan ganin ya ci gaba da taka leda na wasu shekaru masu zuwa, amma tauraron ya nuna cewa zuciyarsa ce za ta ba shi umarni na ƙarshe.
Wannan shekara tana da muhimmanci kwarai ga Neymar, ba wai kawai ga ƙungiyarsa ta Santos ba, har ma da ƙasar sa ta Brazil. Kasancewar akwai gasar cin kofin duniya World Cup a gaba, Neymar ya bayyana hakan a matsayin babban ƙalubale da yake son fuskanta kafin ya kai ga yanke shawara ta ƙarshe.
Burinsa shi ne ya tabbatar ya bar tarihi mai kyau a wannan gasa, wacce yake gani a matsayin dama ta ƙarshe don tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jaruman Brazil.
Dangane da yanayin jikinsa kuwa, Neymar ya bayyana dalilin da ya sa ya zauna a wasu wasannin na wannan kakar, inda ya ce burinsa shi ne ya dawo yana jin kansa 100%.
Ya soki masu maganganun banza da ba su san halin da yake ciki na yau da kullum ba, yana mai cewa dole ne ya jure wa waɗannan surutai don cimma burinsa na dawowa fili ba tare da jin tsoro ko ciwo ba. Wannan jinkiri ya kasance wani mataki na kariya don tabbatar da cewa ba zai sake samun rauni mai tsanani ba.
Neymar ya jaddada cewa babban burinsa shi ne ya taimaka wa ƙungiyarsa, amma ya zaɓi ya dakata har sai ya samu cikakken ƙarfi da karsashi.
Ya bayyana cewa yana buƙatar samun karsashi da gogewa a wasanni a hankali, kuma ta hanyar juriya ne kawai zai iya kaiwa ga matakin da yake buƙata.
A yanzu, yana tafiya ne mataki-mataki, yana lura da yadda jikinsa yake amsawa kafin ya yanke hukunci kan makomarsa a filin wasa.
A ƙarshe, tauraron ya bayyana cewa ba zai iya faɗin takamaiman abin da zai faru a nan gaba ba, domin zai bi abin da zuciyarsa ta gaya masa ne. Rana ɗaya bayan ɗaya nake ɗaukar abin, in ji Neymar, yayin da yake nuna cewa rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa tana matakin da komai na iya faruwa a kowane lokaci.
Wannan labari ya bar daukacin masoya kwallon kafa da fargaba da kuma jiran ganin yadda wannan babban babi na tarihin Neymar zai kare a karshen shekarar nan.

Comments
Post a Comment