Shugaban Kamfanin BUA Ya Yi Alkawarin Fiye da Dala Miliyan 1.5 Ga ‘Yan Wasan Super Eagles
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 10 ga Janairu, 2026, Rabiu ya yi alkawarin dala 500,000 ga tawagar Super Eagles idan suka samu nasara a wasan semi-final. Haka kuma, ya ƙara da alkawarin dala 50,000 kan kowanne ƙwallo da tawagar za ta ci a wannan wasa.
Ba a nan ya tsaya ba, domin ya kuma sha alwashin bayar da dala 1,000,000 idan Super Eagles suka lashe wasan ƙarshe na gasar, tare da ƙarin dala100,000 kan kowanne ƙwallo da za su ci a wasan.
Wannan kyauta ta jawo yabo daga ‘yan Najeriya da masu sha’awar kwallon kafa, inda da dama ke kallon hakan a matsayin ƙarin kwarin guiwa da goyon bayan ƙasa ga tawagar kwallon kafa.
Yayin da Super Eagles ke ci gaba da shirin tunkarar wasan semi-final, wannan goyon baya daga Alhaji Rabiu na nuna irin yadda ‘yan Najeriya ke marawa tawagar baya tare da fatan ganin an ɗaga kofin nahiyar Afrika a karo na huɗu.

Comments
Post a Comment