Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Kwashe Sojoji Zuwa Guinea Bissau
Rundunar sojin saman Nijeriya ta fara gudanar da kwashe kashi na farko na tawagar sojojinta da za su shiga sahun rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar ECOWAS a kasar Guinea Bissau (ESCB).
Wannan mataki na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da daukar matakan tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka, inda Nijeriya ke ci gaba da taka rawar gani wajen jagorantar samar da zaman lafiya.
Rundunar ta tabbatar da gudanar da wannan aiki ne ta wani sakon da ta fitar a shafinta na hukuma a ranar Asabar, inda ta bayyana cewa an tura jami'an ne domin su cika mukamansu a karkashin tsarin kungiyar ta ECOWAS. Wannan turawa na nuni da kudirin Nijeriya na ci gaba da bayar da goyon baya ga kasashen da ke fuskantar kalubalen tsaro ko kuma bukatar karfafa tsarin mulkin demokradiyya a yankin.
Ana sa ran wadannan sojoji za su yi aiki kafada da kafada da sauran takwarorinsu na kasashen yankin don tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar ta Guinea-Bissau. Hakan zai kuma kara daukaka sunan Nijeriya a matsayin jagora wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a nahiyar Afrika.

Comments
Post a Comment