Ministocin kuɗi da na gidaje sun yi murabus da kansu, yayin da Ministan wutar lantarki ma ya ajiye aiki don takarar Gwamna
Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar da bayani na musamman don fayyace yanayin da ya kai ga barin aikin wasu manyan ministoci a majalisar zartarwa ta tarayya.
Sanarwar ta tabbatar da cewa tsohon Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, da tsohon Ministan Gidaje da Bunkasa Birane, Ahmed Musa Dangiwa, sun ajiye ayyukansu ne da kansu ba tare da an kore su ba.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin sake tsarin gudanarwa don tunkarar ƙalubalen tattalin arziki da ke gaban ƙasa.
A gefe guda, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, shi ma ya mika takardar murabus ɗinsa ga Shugaban Ƙasa. Dalilin ajiye aikin nasa ya fito fili, inda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Oyo a zaɓe mai zuwa.
Adelabu ya nuna cewa yana son komawa jiharsa don bayar da gudunmawa kai tsaye ga al'ummarsa, bayan ya kwashe lokaci yana jagorantar ɓangaren wutar lantarki na ƙasa wanda ke fuskantar gyare-gyare daban-daban.
Murabus ɗin wadannan ministoci ya haifar da cece kuce a fadin ƙasar, musamman game da yadda ayyukan ma'aikatunsu za su ci gaba da gudana ba tare da tangarda ba.
Mista Wale Edun ya kasance jigo a shirye-shiryen farfaɗo da darajar Naira da kuma tsarin raba tallafi ga masu ƙananan ƙarfi. Haka ma, Ahmed Musa Dangiwa ya taka rawar gani wajen samar da tsare-tsaren gidaje masu sauƙin kuɗi ga ma'aikata, wanda hakan ya sa barinsu aikin ya zama babban gibi a cikin gwamnatin.
Fadar Shugaban Ƙasa ta gode wa ministocin bisa sadaukarwa da kishin ƙasa da suka nuna a tsawon lokacin da suka kwashe suna hidima. Shugaban ya jaddada cewa gudunmawar da suka bayar za ta kasance ginshiƙi ga duk waɗanda za su gaje su.
A halin yanzu, ana ranar shugaban zai mika sunayen sabbin ministoci ga Majalisar Dattawa domin tantancewa don tabbatar da cewa babu tsaiko a cikin gudanar da manyan ayyukan da waɗannan ma'aikatu suka sa gaba.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa murabus ɗin na Adelabu don yin takara na nuna yadda siyasar shekarar 2027 ke fara ɗaukar zafi tun yanzu.
Yayin da ake jiran sanar da sabbin fuskoki, 'yan ƙasa suna zura ido don ganin ko waɗanda za a naɗa za su iya dorewa da manufofin tattalin arziki da gyaran wutar lantarki da aka riga aka fara. Wannan sauyi na nuna cewa gwamnati na iya fuskantar sabon salo na gudanarwa a watanni masu zuwa.

Comments
Post a Comment