Dole Kamfanonin Sadarwa Su Biya Masu Amfani da Layi Diya Kan Rashin Kyawun Sabis

 

Hukumar Sadarwa ta Ƙasa NCC ta fitar da wani sabon umarni mai ƙarfi wanda ya fara aiki a wannan watan na Afrilu, 2026, inda ta wajabta wa duk kamfanonin sadarwa na ƙasar nan su biya masu amfani da layi diyya duk lokacin da aka samu matsalar sabis. 

Wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafe da dama da jama'a suka yi kan yadda ake yawan samun katsewar kiran waya, jinkirin aika saƙonni, da kuma rashin saurin intanet. Hukumar ta bayyana cewa ba za ta ƙara amincewa da yanayin da mutane ke biyan kuɗi amma ba sa samun ingantaccen abin da suka biya ba.

A ƙarƙashin wannan sabon tsari, kamfanonin sadarwa dole ne su rinka mayar wa masu amfani da layi kuɗinsu ko kuma ba su kyautar lokacin magana  da zarar an tabbatar da cewa an samu matsala daga ɓangaren kamfanin. 

Misali, idan aka samu katsewar kiran waya ba gaira ba dalili, ko kuma idan intanet ya daina aiki na wani lokaci mai tsawo, kamfanin yana da nauyin sanar da abokan cinikinsa da kuma ba su wani abu a matsayin diyya. 

Wannan zai tilasta wa kamfanonin zuba jari wajen gyara kayayyakin aikinsu domin guje wa asarar da za su yi idan suka ci gaba da ba da sabis maras kyau.

Hukumar NCC ta kuma bayyana cewa ta samar da wata na’ura ta musamman da za ta rinka sanya ido kan ingancin sabis ɗin kowane kamfani a kowane yanki na Najeriya. 

Wannan zai ba hukumar damar gano inda aka samu matsala ba tare da sai abokan ciniki sun kai ƙara ba. Duk kamfanin da aka samu yana saɓa wa wannan sabuwar doka ko kuma yake ƙoƙarin kauce wa biyan diyya, zai fuskanci tara mai tsanani ko kuma wasu matakai na hukunci waɗanda za su iya shafar lasisin gudanar da kasuwancinsa.

Wannan mataki ya samu kyakkyawar taraba daga ƙungiyoyin kare haƙƙin masu amfani da yanar gizo da wayar salula a faɗin ƙasar. Suna ganin cewa wannan ita ce hanya mafi dacewa ta sa kamfanonin sadarwa su rinka daraja abokan cinikinsu. 

A baya, masu amfani da layi kan yi asarar bayanai ko lokacin magana saboda matsalar na’ura ba tare da an mayar musu da komai ba, amma yanzu wannan doka za ta ba su kariya tare da tabbatar da cewa ana samun adalci a harkar kasuwancin sadarwa.

A ƙarshe, NCC tana kira ga dukkan masu amfani da wayar salula da su kasance masu lura da yanayin sabis ɗinsu sannan su rinka kai rahoton duk wata matsala da suka fuskanta ga kamfanoninsu ko kuma kai tsaye ga hukumar idan ba su sami gamsuwa ba. 

Manufar wannan doka ita ce bunkasa tattalin arzikin zamani ta hanyar samar da ingantacciyar hanyar sadarwa wadda za ta taimaka wa ’yan kasuwa da sauran jama’a gudanar da ayyukansu cikin sauƙi ba tare da fargabar asarar kuɗi ko lokaci ba.


Comments

Popular posts from this blog

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Syria: Sabon Matakin Diflomasiyya tsakanin Gwamnati da Mayaƙan Ƙurɗawa

Wani ɗan asalin Ireland ya shiga rikici a wata ƙasa – Gwamnatin Ireland na sa ido kan lamarin

Saudi Arabia da Najeriya Sun Kulla Yarjejeniyar Daukar Ma’aikata