Bikin Cika Shekaru 75: Shugaba Tinubu Ya Juna wa Gidan Rediyon Nigeria (FRCN) Juna
A yau Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2026, babbar hanyar yaɗa labarai ta ƙasa, wato Gidan Rediyon Nigeria (FRCN), take bikin cika shekaru 75 da kafuwar ta.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura saƙon taya murna ga shugabanni da ma’aikatan hukumar, inda ya bayyana FRCN a matsayin muryar da ta haɗa kan ‘yan Nigeria tun daga lokacin mulkin mallaka har zuwa yau. Shugaban ya jaddada cewa wannan gidan rediyo ya taka rawar gani wajen adana tarihin ƙasar nan da kuma samar da sahihan bayanai ga jama'a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa FRCN ita ce cibiyar yaɗa labarai mafi girma a nahiyar Afirka, tana da gidajen rediyo na FM guda 47 da kuma shiyyoyi shida. Shugaban ya yaba da yadda hukumar take amfani da yarukan gida wajen isar da saƙonni zuwa karkara, wanda hakan ya taimaka ƙwarai wajen wayar da kan jama’a game da manufofin gwamnati da kuma zaman lafiya.
Baya ga haka, Shugaban ƙasar ya bayyana cewa FRCN ta zama makarantar horar da ƙwararrun ma’aikata, inda ta samar da fitattun masu gabatar da shirye-shirye da injiniyoyin sauti waɗanda aka sani a faɗin duniya. Ya ce hukumar ta kasance wata babbar majigi wadda ke nuna al'adu da rayuwar 'yan Nigeria daban-daban, tana ƙarfafa zumunci a tsakanin kabilu da addinan ƙasar nan ta hanyar shirye-shiryenta na ilimantarwa da nishaɗantarwa.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, shima ya taya hukumar murna, inda ya nuna yadda Rediyon Nigeria ya taimaka wajen yaƙi da ra'ayin tsagera da kuma wanzar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas. Gwamnan ya bayyana cewa amfani da harshen gida da rediyon yake yi ya taimaka wa mutanen karkara wajen samun labarai na gaskiya, wanda hakan ya rage tasirin labaran ƙarya da ke raba kan al'umma.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya buƙaci ma’aikatan FRCN da su ci gaba da riƙe taken hukumar na Wato Ciyar da Jama'a Gaba da Haɗa Kan Ƙasa. Ya ƙarfafa musu gwiwa da su rungumi sabbin fasahohin zamani na intanet domin tabbatar da cewa muryar Nigeria ta ci gaba da tashi a dukkan sassan duniya, musamman a wannan lokaci da duniya ta zama ƙauye ɗaya.

Comments
Post a Comment