Gwamnatin Tarayya Ta Janye Takunkumin Shigo Da Man Fetur Duk Da Adawar Dangote

 

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanar da janye haramcin shigo da man fetur daga ƙasashen ƙetare, inda ta amince da ba wa wasu kamfanoni shida lasisin shigo da man. Wannan mataki ya zo ne a jiya kwanaki kaɗan bayan da aka dakatar da bayar da irin wannan lasisi don bai wa matatar man Dangote damar mamaye kasuwar gida. Sai dai wannan sabon hukunci ya fuskanci adawa mai ƙarfi daga mahukuntan matatar, waɗanda ke ganin matakin a matsayin wata barazana ga ci gaban masana’antun cikin gida.

A nata ɓangaren, matatar man Dangote ta bayyana cewa matsaloli da rashin inganci a tsarin nan na naira domin d'anye suna yi mata cikas. Kamfanin ya koka da cewa baya samun isasshen danyen man da aka yi yarjejeniya a kai, wanda hakan ke rage karfin matatar na samar da isasshen man fetur din da zai biya buƙatun ƴan Nijeriya a cikin gida. Shugabannin matatar sun jaddada cewa ba tare da danyen mai ba, ba za su iya tabbatar da wadatar mai a faɗin ƙasar ba.

Hukumomin Nijeriya sun bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne saboda ƙarancin man da aka fara fuskanta da kuma rashin tabbas a kasuwannin duniya sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya. Don kauce wa tsadar rayuwa da dogon layi a gidajen mai, gwamnati ta ga dacewar buɗe kofofin shigo da mai don cike gibin da aka samu. Wannan mataki na nufin tabbatar da cewa ƙasar ba ta rasa man fetur ba a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.

Rahotanni sun nuna cewa, kwanaki kaɗan da suka gabata, matatar man ta Dangote ta yi barazanar cewa za ta fara fitar da dukkan kayayyakin da take samarwa zuwa ƙasashen waje idan har gwamnati ba ta daina bayar da lasisin shigo da mai ba. Dangote ya yi zargin cewa shigo da man yana durƙusar da darajar abubuwan da suke samarwa a gida, kuma zai gwammace ya sayar da man sa a kasuwannin duniya inda zai sami riba fiye da ya zauna yana gasa da man da ake shigowa da shi.

Wannan takaddama tsakanin gwamnati da matatar Dangote ta haifar da fargaba a tsakanin masana tattalin arziki game da makomar wadatar man fetur a Nijeriya. Yayin da gwamnati ke kokarin ganin man ya wadatu ta hanyar shigo da shi, masu ruwa da tsaki a fannin man fetur na kira da a zauna a tattauna don warware matsalolin da ke damun matatun cikin gida. Masu sharhi na ganin cewa dorewar wannan tsari ya dogara ne ga yadda aka daidaita tsakanin bukatun masu zuba jari da kuma kiyaye harkar man fetur daga rugujewa.

Comments

Popular posts from this blog

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Syria: Sabon Matakin Diflomasiyya tsakanin Gwamnati da Mayaƙan Ƙurɗawa

Wani ɗan asalin Ireland ya shiga rikici a wata ƙasa – Gwamnatin Ireland na sa ido kan lamarin

Saudi Arabia da Najeriya Sun Kulla Yarjejeniyar Daukar Ma’aikata