Shugaba Tinubu Ya Nada Tunji Disu A Matsayin Sabon Shugaban ’Yan Sanda Bayan Murabus Din Egbetokun
A ranar Talata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, biyo bayan takardar ajiye aiki da ya mika wa fadar shugaban kasa.
Egbetokun ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne saboda wasu dalilai na kashin kansa da suka shafi iyalinsa, wadanda suka bukaci ya janye daga nauyin dake kansa a yanzu.
Shugaba Tinubu ya karbi murabus din tare da mika sakon godiya ga Egbetokun bisa jajircewarsa wajen gudanar da sauye-sauye a rundunar tun bayan rantsar da shi a watan Yunin 2023, inda ya yaba da irin gudunmuwar da ya bayar wajen inganta tsaron cikin gida.
Domin kauce wa gurbataccen tsari a shugabancin rundunar, Shugaba Tinubu ya amince da nada Mataimakin Sufeto Janar AIG Tunji Disu a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda Ag. IGP ba tare da bata lokaci ba.
Tunji Disu, wanda kwararren jami’i ne dake da gogewa ta musamman wajen yaki da manyan laifuka, ya taba rike mukamai daban-daban ciki har da shugabancin rundunar binciken manyan laifuka ta IRT da kuma Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Rivers.
Ana kallon nadin nasa a matsayin matakin da zai kawo sabon jini da karsashi a kokarin da gwamnati ke yi na dakile garkuwa da mutane da fashi da makami.
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an yi wannan nadi ne bisa bin ka’idojin shari’a da kuma kwarewar da Disu ya nuna a tsawon shekarunsa na aiki.
Sanarwar ta jaddada cewa shugaba Tinubu ya amince da Disu ne saboda amincewa da kwarewarsa wajen amfani da fasahar zamani da dabarun leken asiri wajen gano masu laifi.
Wannan canji na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro a shiyyoyi daban daban, wanda hakan ke bukatar shugabanci mai karsashi da kuma sanin makamar aiki kamar yadda aka san Disu da shi.
Bisa tanadin Dokar ’Yan Sanda ta shekarar 2020, Shugaban Kasa zai kira taron Majalisar ’Yan Sanda ta Kasa Nigeria Police Council nan ba da jimawa ba domin tabbatar da nadin Tunji Disu a hukumance.
Wannan majalisa, wacce ta kunshi Gwamnonin jihohi 36 da sauran manyan masu ruwa da tsaki, ita ce ke da alhakin tantancewa da kuma amincewa da nadin Sufeto Janar kafin ya zama na din din din.
Bayan kammala wannan mataki, za a mika sunan Disu ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da kuma rantsar da shi a matsayin babban jami’in da zai jagoranci ’yan sandan Najeriya.
Wannan sauyi na shugabanci ya haifar da tsammani mai girma daga wajen ’yan Najeriya wadanda ke fatan ganin an kawo karshen tashe tashen hankula.
Tunji Disu ya shahara wajen hulda mai kyau da farar hula da kuma kokarin sa ido kan ayyukan jami’ai don kauce wa cin zarafin bill adama, wanda hakan ke zama babban kalubale ga rundunar.
Yayin da yake karbar ragamar mulki, babban aikin dake gaban sabon Mukaddashin Sufeto Janar shi ne hada kan jami’an rundunar da kuma samar da sabbin dabarun da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a fadin tarayyar Najeriya.

Comments
Post a Comment