Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya Na Joy Ngozi Ezeilo Ta Bayyana Mummunan Halin Da Mata Ke Ciki A Sudan
Farfesa Joy Ngozi Ezeilo, ɗaya daga cikin manyan jami’an bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya, ta fito fili ta yi ƙarin haske kan sakamakon binciken da suka gudanar game da ayyukan dakarun RSF a Sudan.
A matsayinta na mamba a kwamitin gano gaskiya, ta bayyana cewa shaidun da suka tattara daga bakin mutanen da suka kuɓuta abin ban tsoro ne.
Bayanan sun nuna yadda ake keta haƙƙin bil'adama ta hanyar amfani da fyade da cin zarafin mata a matsayin makamin yaƙi don tsoratar da fararen hula.
Misis Ezeilo ta jaddada cewa dakarun RSF sun kafa wasu sansanoni na musamman inda suke tsare da mata da ‘yan mata a matsayin bayin jima'i. Shaidun da aka samu daga waɗanda suka tsira sun nuna cewa ana yi wa mata fyaɗe a gaban iyalansu, sannan ana kwashe su zuwa wuraren da ba a sani ba.
Wannan bincike ya tabbatar da cewa ba wai kawai abubuwan suna faruwa ba ne lokaci zuwa lokaci, a’a, wani tsari ne da aka riga aka tsara don ruguza mutuncin al’ummomin da dakarun ke mamayewa.
Haka kuma, jami’ar ta bayyana yadda dakarun ke amfani da barazanar kisa don hana mutane magana ko neman taimako. Yawancin matan da suka yi magana da kwamitin binciken sun bayyana cewa sun rasa gidajensu da rayukan ‘yan uwansu kafin a tafi da su.
Ezeilo ta nuna damuwa kan yadda yanayin tsaro ya sa yake da wahala ga kungiyoyin agaji su kai wa waɗannan mata ɗauki, wanda hakan ke ƙara tsananta raunin da suka ji na jiki da na zuciya.
Binciken ya kuma karkata ne ga yadda ake fataucin mutane a yankunan da RSF ke iko da su. Joy Ngozi Ezeilo ta ce akwai kwararan shaidu da ke nuna cewa ana sayar da wasu matan ko kuma a kai su wasu sassa na daban don bautar da su.
Wannan ya saba wa dukkan dokokin kasa da kasa na kare hakkin dan adam, kuma tana kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar mataki domin kawo karshen wannan rashin imanin da ake yi wa bayin Allah a kasar Sudan.
A ƙarshe, Ezeilo ta buƙaci kotun manyan laifuka ta duniya ICC da sauran hukumomin shari'a da su yi amfani da waɗannan hujjoji don gurfanar da shugabannin RSF.
Ta bayyana cewa yin shiru ga irin waɗannan laifuka zai sa masu aikatawa su ci gaba da cin karensu ba babbaka. Burin kwamitin binciken shi ne ganin an tabbatar da adalci ga duk wadanda abin ya shafa da kuma samar da hanyoyin tallafa wa rayuwar matan da suka samu kansu a cikin wannan hali.

Comments
Post a Comment