Hukumar FRSC Ta Sallami Ma'aikata 43 Saboda Karya Ka'idojin Aiki da Rashin Ɗa'a


A yayin da Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Hurda da jama'a ta ƙasa FRSC, Mallam Shehu Mohammed, ya sanar da sallamar ma'aikatan hukumar guda 43 a hukumance a ranar Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026. 

Wannan mataki ya shafi jami’an da aka samu da laifuka daban daban da suka haɗa da guduwa daga wurin aiki, halayen da ba su dace da tarbiyyar hukumar ba, da kuma saɓawa ƙa’idojin aiki yayin gudanar da sintiri a kan hanyoyi. Babban Kwamandan ya bayyana matakin a matsayin tabbaci mai ƙarfi na manufar hukumar ta ƙin lamuntar rashin ɗa’a.

Mallam Shehu Mohammed ya bayyana cewa, daga cikin ma'aikatan da aka kora, mutum 31 an same su da laifin guduwa daga bakin aiki, yayin da mutum 5 suka nuna halayen da suka ɓata martabar hukumar, sauran mutum 7 kuma sun tafka kura kurai yayin sintiri. 

Ya kara da jaddada cewa kowane jami’in FRSC yana wakiltar martaba da mutuncin hukumar ne a idon duniya, don haka duk wanda ya zaɓi ya kauce wa tsarin aikin zai fuskanci fushin hukunci ba tare da sassauci ba.

A cewar Babban Kwamandan, wannan mataki wani saƙo ne ga dukkan sauran jami’an hukumar cewa shekarar 2026 shekara ce ta dawo da karsashi, kwarewa, da kuma inganta ayyukan hukumar. 

Ya bayyana cewa hukumar ba za ta bar duk wani abu da zai raunana amincewar da al’umma suke da ita ga jami'an FRSC ba, musamman ma a wannan lokaci da ake ƙoƙarin rage haɗuran hanyoyi ta hanyar amfani da dabarun aiki na zamani.

Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da hukumar take ƙarfafa sa ido kan jami'anta a faɗin ƙasar. 

Mallam Shehu Mohammed ya umurci kwamandojin shiyyoyi da na jihohi da su riƙa sanya ido sosai kan yadda ma'aikatansu suke gudanar da ayyukansu, inda ya ce rashin ɗa'a ba zai ƙara samun mafaka a ƙarƙashin kayan sarki na FRSC ba. 

Ya ƙara da cewa za a ci gaba da ba da muhimmanci ga jin daɗin ma'aikata, amma hakan ba zai hana hukunta duk wanda ya tafka kuskure ba.

A ƙarshe, Babban Kwamandan ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hukumar FRSC za ta ci gaba da kasancewa ƙungiyar da ke aiki da kwarewa da gaskiya. 

Ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da ba jami'an hukumar haɗin kai, tare da bayar da rahoton duk wani jami'i da aka gani yana aikata ba daidai ba. Wannan mataki na korar ma'aikatan ana ganinsa a matsayin wani babban juyi da zai sake gyara fasalin aikin hukumar a wannan sabuwar shekara.


Comments

Popular posts from this blog

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Syria: Sabon Matakin Diflomasiyya tsakanin Gwamnati da Mayaƙan Ƙurɗawa

Wani ɗan asalin Ireland ya shiga rikici a wata ƙasa – Gwamnatin Ireland na sa ido kan lamarin

Saudi Arabia da Najeriya Sun Kulla Yarjejeniyar Daukar Ma’aikata