Kotu Ta Umarci Kwace Kadarorin da Suka Kai Naira Biliyan 213 da Aka Danganta da Tsohon Minista Abubakar Malami
A zaman shari’ar da aka yi yau Laraba a babban kotun tarayya da ke Abuja, mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarni na ƙwace kadarori da dama da suka haɗa da filaye, makarantu, gidajen mai, da sauran kadarori da darajarsu ta kai kusan naira biliyan 213.
Kadarorin da aka bayar da umarnin ƙwacewa an danganta su da tsohon ministan shari’a na ƙasa, Abubakar Malami. Hukumar EFCC ce ta shigar da buƙatar ƙwace kadarorin bisa zargin mallaka ba bisa ka’ida ba da kuma almundahana yayin da Malami ke rike da muƙaminsa.
A yayin zaman kotun, lauyoyin Malami sun nemi a saurari hujjoji da ke hannunsu, amma alkali Emeka Nwite ya gargade su da cewa ba za a yarda a kawo masa latsi ba ko wata hanya ta neman jinkiri da ba ta dace ba. Sai dai lauyoyin sun jaddada cewa ba su da niyyar yin hakan.
Mai shari’a ya jaddada cewa umarnin ƙwace kadarorin zai ci gaba da aiki har sai an kammala bincike da kuma shari’a kan asalin kadarorin da hanyoyin da aka bi wajen mallakarsu. Ya kuma bukaci EFCC ta ci gaba da gabatar da shaidu a matakin gaba.
Wannan hukunci na daga cikin matakan da ake dauka don karfafa yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, tare da tabbatar da cewa duk kadarorin da aka mallaka ba bisa ka’ida ba za su dawo hannun gwamnati.

Comments
Post a Comment