Gwamnatin Najeriya ta yi wa masu yunƙurin juyin mulki fatattakar kare a ƙasar Benin

 


DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Najeriya ta yi wa masu yunƙurin juyin mulki fatattakar kare a ƙasar Benin


Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ɗauki matakin magance wata ƙungiya da ake zargin tana shirya yunƙurin juyin mulki daga makwabciyar ƙasar Benin, domin kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron Najeriya.


Gwamnatin Benin ma ta tabbatar da cewa tana aiki kafada da kafada da Najeriya wajen kawo ƙarshen duk wata barazana a yankin. Ta sha alwashin ba za ta bar ƙasarta ta zama mafakar masu tada zaune tsaye ba.


A halin yanzu, hukumomin tsaro sun umarci al’umma da su kasance cikin shiri tare da bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen kare ƙasar daga duk wani hare-hare. Gwamnati ta ce za ta ci gaba da daukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.


Comments

Popular posts from this blog

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Syria: Sabon Matakin Diflomasiyya tsakanin Gwamnati da Mayaƙan Ƙurɗawa

Wani ɗan asalin Ireland ya shiga rikici a wata ƙasa – Gwamnatin Ireland na sa ido kan lamarin

Saudi Arabia da Najeriya Sun Kulla Yarjejeniyar Daukar Ma’aikata