Ganduje Ya Janye Yunkurin Kafa Rundunar Hisba Fisabilillah a Kano
Ganduje ya bayyana cewa manufar rundunar ita ce taimakawa wajen yaki da laifuka da kuma inganta tarbiyya a cikin al’umma, musamman a yankunan da hukumomin tsaro ba sa iya kaiwa cikin sauki. Sai dai tuni mutane da dama da masu ruwa da tsaki suka fara bayyana damuwa, suna ganin wannan yunkuri na iya haifar da rudani da kuma rikici da hukumomin tsaro na gwamnati.
Bayan jin koke-koke da shawarwari daga shugabanni, masana harkokin tsaro, da shugabannin addini, Ganduje ya ce ya yanke shawarar janye shirin domin kaucewa rikici ko samun rashin fahimta a tsakanin jama'a. Ya kara da cewa ba ya son wani abu da zai haifar da barazana ga zaman lafiya da hadin kan al'umma, musamman a jihar Kano.
A martanin wasu daga cikin jama’ar jihar Kano, da dama sun yaba da wannan mataki na janye rundunar, suna masu cewa abu ne mai kyau a nemi mafita tare da hukumomi fiye da kafa sabbin ƙungiyoyin da ba su da tushe a doka. Wasu kuma sun bayyana takaici da cewa an janyo hayaniya a kan wani abu da ba a tsara shi yadda ya kamata ba.
Tsohon gwamnan ya kuma bukaci matasa da sauran masu kishin jihar da su ci gaba da tallafawa zaman lafiya da doka ta hanyar aiki tare da hukumomi da kuma rungumar hanyoyin da suka dace don gyara al'umma.

Comments
Post a Comment