Firaministan Libiya ya tabbatar da rasuwar babban hafsan sojin ƙasa a haɗarin jirgin sama a Turkiyya

 


Firaministan gwamnatin rikon kwarya ta Libiya, Abdulhamid Dbeibeh, ya tabbatar da cewa babban hafsan sojojin ƙasar, Muhammad Ali Ahmad al-Haddad, ya rasu tare da wasu mutane huɗu a wani mummunan haɗarin jirgin sama da ya faru a kusa da babban birnin Ankara na ƙasar Turkiyya. 


Haɗarin ya faru ne yayin da jami'an ke kan tafiya ta aiki a cikin wani jirgin sama na musamman. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne a wani yanki da ke kusa da filin jirgin saman Ankara, inda jami’an ceto suka garzaya amma ba su samu ceto rai ba.


Firaminista Dbeibeh ya bayyana alhinin sa tare da mika ta’aziyya ga dangin mamatan da daukacin rundunar sojin Libiya. Ya ce al-Haddad babban jarumi ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.


Rahotanni daga gwamnatin Turkiyya sun nuna cewa an fara bincike kan musabbabin haɗarin jirgin, domin tantance ko akwai matsala ta fasaha ko kuma wani abu daban. An kuma tabbatar da cewa Turkiyya za ta haɗa gwiwa da hukumomin Libiya wajen gudanar da cikakken bincike.


Rasuwar al-Haddad babban gibi ne ga rundunar tsaron Libiya da ƙasar baki ɗaya, musamman a wannan lokaci da ake kokarin kawo karshen rikice-rikicen siyasa da tsaro a yankin.

Comments

Popular posts from this blog

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Syria: Sabon Matakin Diflomasiyya tsakanin Gwamnati da Mayaƙan Ƙurɗawa

Wani ɗan asalin Ireland ya shiga rikici a wata ƙasa – Gwamnatin Ireland na sa ido kan lamarin

Saudi Arabia da Najeriya Sun Kulla Yarjejeniyar Daukar Ma’aikata