Attajirin Mafi Kuɗi a Afirka Ya Zargi Farouk Ahmed da Cin Hanci a Batun Kuɗin Makaranta
A wani lamari da ke ƙara jawo cece-kuce a Najeriya da ma sassan Afirka, attajirin da aka fi sani da mafi arziki a nahiyar, Aliko Dangote, ya zargi Farouk Ahmed babban jami’in gwamnati a harkar man fetur da amfani da kuɗaɗen jama’a wajen biya wa ’ya’yansa huɗu kuɗin makarantar sakandire a ƙasar Switzerland da ya kai dalar Amurka miliyan 5 ($5 million).
Rahotanni sun nuna cewa Dangote ya bayyana wannan zargi ne yayin wata ganawa da kwamitin bincike na majalisa, inda ya ce akwai alamun almundahana da cin hanci da ke faruwa a manyan hukumomin gwamnati, musamman ma a sashen man fetur. Ya bayyana damuwa kan yadda ake karkatar da kuɗin da ya kamata a yi amfani da su wajen cigaban al’umma zuwa bukatun kashin kai.
Makarantun da ’ya’yan Farouk Ahmed ke halarta a Switzerland na daga cikin mafi tsada a duniya, inda kuɗin makaranta ke kai dubban daloli a shekara. Zargin ya jawo suka daga kungiyoyin farar hula da na sa ido kan harkokin gwamnati, suna kiran da a gudanar da cikakken bincike.
Sai dai a nata bangaren, ofishin Farouk Ahmed ya musanta zargin, yana mai cewa ba a taba amfani da kuɗin gwamnati wajen biyan irin waɗannan kudade ba. Sun ce wannan yunkuri ne na bata suna da gangan, kuma za su dauki matakin shari’a idan bukatar hakan ta taso.
Hukumar EFCC da ICPC na duba yiwuwar bude bincike kan batun, musamman idan aka samu sahihan bayanai. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara matsa lamba ga gwamnati da manyan jami’ai su kasance masu gaskiya da rikon amana.

Comments
Post a Comment