An Bukaci Kwamishin 'Yan Sandan Kano Ya Kama Ganduje Kan Yunkurin Kafa Hukumar Hizbah
Wata Kungiya masu rajin mare dimokradiya, wato 'Action Advocay for Democracy and Good Governance' ta yi kira da babban murya ga kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano da a kama tare da turfanar da Dr Abdullahi Umar Ganduje akan yunkurin kafa rundunar Hisbah mai zaman kanta a jihar Kano.
Kungiyar karkashin shugabancin Rabi'u Usman, ta nuna rashin jin dadinsu akan yunkurin Dr Abdullahi Umar Ganduje na kafa rundunanar tsaro na Hisbah mai zaman kanta.
Kungiyar ta kara da cewa, abin da ya dace da Ganduje shine zaman gidan yari, don girbar abunda ya shuka.
"Wannan yunkuri ne, na ta'addanci kuma yunkuri ne na tada husumiya da rikici a jihar Kano.
Ganduje ya daina tunani kamar karamin yaro, ya kamata ya rika tunani kamar yadda shekarunsa yake a matsayinsa na Dattijo. Kuma tsohon gwamna wanda ya shafe shekuru takwasa a karagar mulki.
Amma Ganduje ba shi da wata manufa saidai ya ga Kano na cikin rudani da kuma tashin hankali.
Mutumin da aka kama dumu-dumu yana saka dala a aljihuunsa tare da kuma zargin wasu badakala na wasu kudade wanda ya saka aka tilasta masa sauka a kujerarsa na shugaban jam'iyyar APC, shine yake ta neman tayar da hankular jama'r jihar Kano", kamar yadda kungiyar ta kara da cewa..
A don haka ne kugiyar take kira ga Shugaban 'yan sandan jihar Kano da su gaggauta kama tare da gurfanar da Ganduje cikin gaggawa kafin ya cimman wannan mummunan kudirinshi na kafa rundunar Hisban masu zaman kansu.

Comments
Post a Comment